Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC Farfesa Attahiru Jega, da tsohon shugaban malaman Katolika a Abuja Cardiac John Onaiyekan, sun shaida wa shugaba Buhari cewa ‘yan Nijeriya su na fuskantar wahalhalu biyu na rashin tsaro da na annobar coronavirus.

Don haka sun bukaci Shugaban ya yi duk abin da zai iya domin magance matsalar tsaro ko da hakan ya na nufin sallamar shugabannin hukumomin tsaro.

Shugabannin biyu sun bayyana haka ne, a cikin wata Makala.

Jawabin dai ya na dauke da sa hannun Jega da Onaiyekan da Janar Martin Agwai da Ambasada Fatima Balla da Farfesa Jibrin Ibrahim, da sauran su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *