Wasu al’ummomin Arewa da ke zama a jihar Edo, sun tabbatar da goyon bayan su ga tazarcen gwamna Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP.

Sakataren Sarkin Hausawan Benin Mohammed Baba, ya ce kuri’un su na jam’iyyar PDP ne a zaben gwamnan da za a yi a jihar Edo.

Hausawan da ke zama a garin Benin, sun ce ba su da zabi illa su goyi bayan PDP a zaben ranar 19 ga watan Satumba na shekara ta 2020.

Ya ce Sanmata Rabi’u Musa Kwankwaso Jakadan su ne, don haka ya bukaci su zabi Gwamna Obaseki kuma hakan za su yi.

Mohammed Baba, ya ce su na daukar Sanata Rabi’u Kwankwaso a matsayin Jagoran su, kuma su na girmama shi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *