Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce Nijeriya ta na lalacewa cikin sauri tare da rabewa a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Obasanjo ya bayyana haka ne, a cikin wata maƙala da ya gabatar yayin wani taron ƙara wa juna sani da ya gudana a Abuja, inda ya ce abubuwan da aka daina jin su a da, yanzu su na sake faruwa ta hanyar buga gangar ƙiyayya da rarraba kawuna.

Ya ce a yau Nijeriya ta na lalacewa cikin sauri da komawa musamman ta fuskar haɗin kai da fuskar tattalin arziki, yayin da ta kasance tamkar Cibiyar Talauci ta duniya.

Obasanjo, ya ce abin farin ciki shi ne, ya lura manyan ƙungiyoyin tuntuɓa biyar mafiya girma su na ƙoƙarin nemo bakin zaren domin kare Nijeriya daga rugujewa, sannan ya yi kira ga masu ruwa da tsaki su haɗa ƙarfi don a ciyar da kasar nan gaba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *