Kamfanin man fetur na kasa NNPC, ya maida martani ga masu sukar matakin cire tallafi da gwamnatin tarayya ta yi, inda ya ce masu hannu da shuni ne ke amfana da tallafin ta hanyar yin cuwa-cuwar da ta wuce kima.

Shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari ya shaida wa manema labarai cewa, nan gaba talaka zai ci ribar janye tallafin da aka yi.

Ya ce Talaka ba shi ke cin ribar janye tallafin ba, idan aka yi la’akari da cewa ba kowa ke da abin hawa ba, amma masu hannu da shuni su ke da motoci da dama, don haka masu kudi ke cin ribar tallafin man, kuma bisa la’akari da yadda talaka kullkum shi ke shan wahala ya sa aka janye tallafin.

Mele Kyari, ya ce idan har ba a janye tallafin man ba, ko shakka ba bu talaka zai cigaba da shan wahala, kuma gwamnati ba za ta iya yin wasu ababen more rayuwa ga al’ummarta ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *