Gwamnatin tarayya ta ce ta na tattaunawa da wasu ‘yan kasuwa domin ta saida masu hannun jari a matatun Mai hudu da Nijeriya ta mallaka.

Sanarwar ta fito ne daga shugaban kamfanin NNPC Mele Kolo Kyari, a lokacin da ya zanta da manema labarai, inda ya ce gwamnatin tarayya za ta saida babban kaso na hannun jarin ta a cikin matatun, ta yadda zai zama ‘yan kasuwa ne ke da ta cewa.

Malam Kyari, ya ce za su kawo tsari ta yadda zai zama kamfanin NNPC ya na da wani kaso kadan ne a cikin hannun jarin matatun.

Ya ce idan aka yi haka, zai zama ‘yan kasuwar da su ka zuba hannun jarin su ne za su dauki alhakin gudanar da duk wasu harkokin tace Mai a matatun hudu.

Mele Kyari, ya ce hakan ya na nufin za a rika samun damar yi wa masu ruwa da tsaki binciken kwa-kwaf, kuma za a fi jin dadin yin aiki da kyau.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *