Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane 259 da ake zargi da aikata laifukka daban-daban a cikin makwanni 6 da suka gabata a fadin jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Habu Ahmad, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Ahmad ya ce an kama mutanen ne daga ranar 23 ga watan Yuli zuwa 8 ga wannan watan da muke ciki, a kokarin da rundunar take na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce an kama mutanen ne a lokuta daban-daban da kuma wurare daban-daban a tsakankanin lokacin.

Rundunar ta kara da cewa ta kama kwalaben lemun kwalba da wa’adin amfaninsu ya kara na kimanin naira dubu dari da 50.

Ahmad ya kara da cewa rundunar ta samu wadannan nasarori ne bisa umurnin shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu, na rage yawaitar aikata laifukka. 

Ya kara da cewa daga cikin wadanda aka kama akwai ‘yan fashi da makami guda 45, masu garkuwa da mutane 8, barayin motoci 14, barayin Keke Napep 7 da kuma barayin mashina 14.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *