Hukumar yaki da masu safarar bil’adama ta Najeriya NAPTIP, ta ce ta kubutar da mutane ‘yan asalin jihar Oyo dubu 1 da 52 daga hannun masu safarar bil’adama.

Shugabar hukumar Dame Okah-Donli, ta bayyana haka a lokacin da take magana a ziyarar da ta kaiwa Olubadan, Oba Saliu Adetunji a fadarsa dake Ibadan.

Ta ce jihar Oyo ta fara shiga sahun jihohi da suka zama matattaran fataucin bil’adama inda ake fataucin manya da yara tare da bautar dasu ta hanyoyi daban-daban.

Okah-Donli, ta ce hukumar ta fito da wasu sabbin shirye-shirye da za ta yi amfani dasu wajen wayar da kan al’umma ta yadda za a dakile yawaitar safarar bil’adama a Najeriya.

Sannan ta nemi giyon bayan sarakunan gargajiya a shirya gangamin wayar da kan al’umma kan illar tauye hakkin mata da kananan yara tun daga matakin farko.

A nasa jawabin Oba Saliu Adetunji, ya yabawa hukumar ta NAPTIP, bisa irin muhimmancin da suke nunawa na bil’adama, wanda a cewarsa shine makasudin kafa hukumar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *