Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da karin sama da naira billiyan 8 domin biyan alawus-alawus na yaki da cutar korona ga ma’aikatan lafiya na Najeriya.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Chris Ngige, ya bayyana haka a lokacin sanya hannu yarjejeniya a wajen taron da aka gudanar tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar likitoci yta Najeriya a Abuja.

Idan dai za a iya tunawa kungiyar likitocin ta shiga yajin aikin sai baba ta gani a dukkanin cibiyoyin kula da lafiya ta tarayya a jihohi, a kokarin ganin an biya musu bukatunsu. 

Daga cikin bukatun da likitocin suka gabatar har da biyan su kudaden horo na dukkanin likitocin da aka ware a kasafin kudin shekarar 2020, da kuma ishoran lafiya da na mutuwa ga dukkanin ma’aikatan lafiya.

Sauran sun hada da biyansu kudaden alawus-alawus din su na yaki da cutar korona na watannin Afrailu, Mayu da Yuni, da alawus na yanayin da suke gudanar da aiki a ciki da albashinsu da suke bi bashi tun a shekarar 2014 zuwa 2015.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *