Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce mutane 65 ne suka rasa rayukansu, wasu da dama suka jikkata baya ga mutane da dama da suka rasa muhallansu.

Majiyoyin sun ce ambaliyar ruwan da ta shafi daukacin kasar daga ranar 7 ga watan Satumba ya nuna cewa mutane dubu dari 3da 29 da dari 958 ne suka rasa mahallansu.

Mutanen da suka rasa rayukansu sun mutu ne sanadiyar gine-ginen gidajen da suka ruguje musu, sai dai 14 daga cikin mutanen sun mutu ne ta hanyar nutsewa a ruwa.  

Wani sakamakon da aka bayar ya bayyana rushewar azuzuwan karatu sama da 60 Masalatai sama da 20 tare da rumbunan adana abinci 448 da kuma rijiyoyin ruwan sha 713.

Wuraren da ambaliyar ta fi shafa sun hada da Maradi, Tahoua, Tillabéri, Dosso da kuma birnin Niamey.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *