Ofishin majalisar dinkin duniya da ke Najeriya ya ce ya fito da wani sabon shirin koyar da dalibai ta hanyar amfani da kafafen radio, domin dinke gibin da aka samu sakamakon bular cutar korona.

Jami’in dake kula da ci gaban harkokin ilimi da agajin gaggawa a karkashin Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya Judith Giwa-Amu, ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da manema labarai a Abuja.

Da take magana kan zagayowar ranar kare harkokin ilimi daga hare-hare, Giwa-Amu, ya ce hare-haren dake shafar bangaren ilimi na shafar rayuwar ‘yan kasa.

Ta ce nakassu ne babba ace wata matsala ta hana yara zuwa makarantu.

Ta ce matakin da sashen da take jagoranta ya dauka shine ba bangaren ilimin kulawar gaggawa ta hanyar koyar da dalibai a kafofin yada labarai, lokaci da kuma bayan cutar korona.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *