Gwamnatin tarayya ta ce ya zama wajibi likitoci masu yajin aiki su yi hakuri da ita a lokacin da take kokari cika musu alkawura da kuma bukatun da suka gabatar.

Ministan lafiya Osagie Ehanire, ya bayyana haka a lokacin da yake magana a wani shiri na talabijin, ya ce wannan ba lokaci ne da ya kamata likotocin su shiga yajin aiki ba.

A ranar Laraban nan ne ministan ya umurci matasa da suka kammala aikin likitanci su yi aiki a wuraren da likotoci masu yajin aikin suka bari, yayin da ake tattaunawa da su dan ganin sun janye yajin aikin.

Ya ce wadanda suka kammala karatun za su yi aiki ne a matsayin masu taimakawa ma’aikatan lafiyan dake aiki a asibitocin ba karbe iko a harkokin lafiyan ba.

Ministan ya ce alhakin ma’aikatar ne ta kula da lafiyan ‘yan Najeriya, tare da basu kulawa ta musamman a duk lokacin da wani bashi da lafiya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *