Babban hafsin sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya ce rundunar sojin na daukar wasu sabbin dabaru domin dakile ayyukan ta’addanci a fadin Najeriya.

Buratai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Jaji dake jihar Kaduna.

Ya ce tun a shekarar 2015 babban burinsa shine ya bunkasa harkokin aikin soji, ta hanyar bada horo na musamman, samar da kayayyakin aiki ta yadda jami’an soji zasu samu kwarin gwiwar gudanar da ayyukansu.

Ya ce an samu ci gaba sosai ta bangaren gudanarwa tun bayan da ya hau kan karagar mulki a shakarar 2015.

Buratai ya ce akwai bukatar manyan jami’an soji su yi amfani da damar da suka samu da kuma kwarewar da suke da ita wajen shawo kan matsalolin tsaro da ake fama dasu a wasu yankunan kasar nan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *