Hukumomi a kasaf Philippines sun kama wasu ‘yan Najeriya 4 bisa hannu a satar makudan kudade ta yanar gizo a wasu bankunan kasar.

Shugaban sashen bincike da gudanar da masu aikata laifukka ta yanar gizo Vic Lorenzo, ya ce ‘Yan Najeriya na daga cikin mutanen da suka yi kutse a bankuna. 

Ya ce ‘yan Najeriyan sun sabawa dokar hana damfara da kutse da kuma satar bayanai ta yanar gizo.

Lorenzo ya ce an gano kutsen da mutanen suka yi ne bayan turawa da karkatar da wasu kudade daga bankin zuwa zuwa asusun ajiyar banki daban-daban.

Hukumomin sun kwace katin cire kudi na bangi na bogi da mutanen ke amfani dasu wajen satar kudaden.

Sai dai ‘yan Najeriyan sun karyata zargin da ake musu, inda suka ce basu san wani abu mai suna kutse ba, kuma sun ce kasar ta Philippines ne domin karatu.

Daya daga cikin su ya ce kudaden da suka cire a bankin kyauta ne da wata kungiyar dalibai a Najeriya ta tura musu, domin bunkasa harkokin iliminsu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *