Shugaban hukumar kula da masu shige da fice ta Najeriya Muhammad Babandede ya gargadi ‘yan Najeriya su guji amfani da takardun bogi, na sata ko kuma wadanda amfaninsu ya kare wajen tafiye-tafiye.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce tuni hukumar ta ankarar da rundunar ‘yan sandan kasa da kasa ta INTERPOL kan ‘yan Najeriya dake amfani da irin wadannan takardu.

Babandede ya ce amfani da irin wadannan takardun za su sa a kama mutane a kasashen ketare.

Ya ce hukumar na kara kaimi wajen kamawa tare da hukunta masu amfani da takardun da ba nasu ba, da kuma wadanda suka amfani da wadanda wa’adin amfaninsu ya kare.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *