Rundunar ‘yan sanda ta jihar Borno, ta gargadi mutane a kan kowace irin zanga-zanga sakamakon karin kudin man fetur da na wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta yi.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Mr. Edet Okon ya fitar, ya ce har yanzu akwai dokar hana zanga-zanga a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.

Rundunar ‘yan sandan, ta ce zanga-zangar za ta iya janyo  matsala a zaman lafiyar da aka shafe tsawon lokaci kafin a same shi a jihar.

Sanarwar, ta ce Rundunar ‘yan sandan ta gano cewa, akwai shirin da wasu kungiyoyi ke yi na kawo karshen zaman lafiyar da aka shafe tsawon lokaci kafin a samu a jihar, ta hanyar gudanar da zanga-zanga saboda karin kudin man fetur da na wutar lantarki da tsarin ma’aikatan gwamnati da ma’aikatan N-Power.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Borno CP Mohammed Ndatsu Aliyu ya yi gargadin cewa, rundunar ba za ta amince a gudanar da irin wannan zanga-zanga ba, saboda za ta iya janyo matsala a zaman lafiyan da jami’an tsaro su ka samar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *