Shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya bukashi shugabannin rundunonin ‘yan sanda da su gudanar da ayyukansu ta hanyar amfani da kwarewa da kishi gabannin zaben kwamnonin Edo da Ondo.

Adamu ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na musamman da aka gudanar da shugabannin shiyoyi na rundunar a Abuja.

Ya ce an kammala shirye-shirye domin turawa da wasu manyan jami’an rundunar domin gudanar da ayyuka na musamman a zabubukan da za su gudana a jihohin Edo da Ondo.

Adamu ya ce rundunar ‘yan sandan, hukumar zabe da sauran hukumomin tsaro za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da sahihin zabe a jihohin.

Sannan ya kara jadda cewa hukumar za ta samar da isassun jami’an ‘yan sanda domin ba masu kada kuri’a cikakkiyar kariyar da ake bukata wajen cin romon demokradiyya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *