Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci shugabannin kungiyar rainon tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS kada su tsawaita wa’adin zama akan karagar mulki sabanin kundin tsarin mulki.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu ya bayyana haka, ya ce shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi a wajen taron kungiyar karo na 57 da ya gudana a Niamey babban birnin kasar Niger.

Shugaba Buhari ya bukaci takwarorinsa na kasashen Afrika su rika mutunta dokokin kasa tare da ba al’ummomin su damar zaben abin da suke so ta hanyar gudanar da sahihin zabe.

Sannan ya yabawa shugaban kungiyar mai barin gado kuma shugaban kasar Nijar kan namijin kokari da ya yi wajen daidaita kasashen dake kungiyar.

Shugaba Buhari ya kuma yabawa jami’in kungiyar mai shiga tsakani, kuma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan bisa irin kokarin da ya yi na ganin an magance rikice-rikicen siyasa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *