Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kalubalanci ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati su yi amfani da sabon tsarin farfado da tattalin arziki domin ragewa ‘yan Najeriya matsalolin dake damun su.

Shugaba Buhari ya bukaci hakan ne a wajen taron bita kan aikace-aikacen ministocin na shekara guda wanda ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Yemi Osinbajo, ya ce ya zama wajibi ministocin da sauran manyan jami’an gwamnati su aiwatar da abubuwan dake gabansu domin jin dadin ‘yan kasa.

Ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da bunkasa harkokin noma da shirin ba manoma bashi karkashin babban bankin Najeriya wanda a cewarsa shine ginshikin bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *