Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ta shawarci gwamnatin tarayya ta kara yin dubi akan karin farashin kudin man fetur da ta yi a cikin wannan makon.

Shugaban hukumar mai kula da shiyyar jihar Adamawa, Augustine Ndaghu, ya bada shawarar a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Yola.

Ndaghu ya ce gwamnatin tarayya ta dauki wannan mataki ne a lokacin da bai kamata ba, duba da irin halin rayuwa da annobar cutar korona ta jefa mutane a ciki.

Ya ce karin kudin man fetur a wannan lokaci zai jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *