Rundunar tsaro ta sojojin Nijeriya, ta ce ta kashe ɗan fashi ɗaya, tare da kama takwas a Jihar Benue, sannan ta kama huɗu tare da karɓe makamai a hare-hare biyu da ta kai.

A cikin wata Sanarwar da ta fitar, ta ce dakarun rundunar Operation Whirl Stroke ne su ka kai hare-haren a Dajin Guma da ke kan iyakar jihohin Benue da Nasarawa, bayan samun wasu rahotannin sirri cewa ‘yan fashin su na zaune a wurin.

A wani samamen na daban, sojojin sun kama wasu mutane huɗu tare da kwace bindigogi ƙirar AK-47 a Gwer da ke jihar Benue, sannan su ka tarwatsa sansanin su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *