Shugaban hukumar kiyaye haɗura ta Jihar Anambra, ya ce fasinjoji sun ƙone ƙurmus sakamakon hatsarin wata mota da ya rutsa da su ta yadda ba za a iya gane su ba.

Mista Andrew Kumapayi ya ƙara da cewa, har zuwa yanzu ba su san takamaiman adadin waɗanda su ka rasa rayukan su ba saboda ƙonewar da su ka yi.

Hatsarin dai ya faru ne a kan titin Ihiala-Onitsha da ke Jihar Anambra, inda motar su ta kama da sakamakon fashewar taya saboda tsananin gudu.

Rahotannin sun bayyana cewa, dukkan fasinjojin sun ƙone ta yadda ba za a iya gane su ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *