Kakakin ma’aikatar tsaro John Enenche, ya yi kira ga mazauna birnin Abuja su kwantar da hankalin su, cewa ana yin binciken zargin da ke cewa mayakan Boko Haram za su afka wa mutane garin.

An dai samu wata takardar sirri daga ofishin hukumar Kwastan ta Ƙasa, inda ta ke gargaɗin mutane cewa an samu rahoton Boko Haram su na kakkafa wasu sansanoni a dazuzzukan da ke kewaye da birnin Abuja, domin shirin afka wa yankunan Abuja da Nasarawa da kuma Kogi.

Da ya ke yi wa manema labarai karin haske,  Kakakin hukumar ya ce bai san da wannan magana ba.

Takardar dai ta ƙunshi wasu wurare da aka ce Boko Haram su na kafa sansanoni kamar haka, wadan da su ka hada da Dajin Kunyam kusa da rukunin gidaje na DIA a Abuja, da Dajin Robochi da ke Gwagwalada, da dajin Kwaku da ke Kuje, da Dajin Unaisha da ke karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa, da Dajin garin Gegu da ke jihar Kogi domin shirin afka wa Abuja.

Sai dai ma’aikatar tsaro ta bukaci mutane su kwantar da hankalin su, cewa jami’an tsaro a tsaye su ke domin samar da tsaro ga mutane baki daya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *