Fadar shugaban kasa ta ce matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na cire tallafin man fetur daidai ne.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Garba Shehu, ya bayyana haka, ya ce matakan da aka ɗauka ne su ka jawo hakan waɗanda kuma sun zama wajibi.

Garba Shehu, ya ce tarihi ba zai taɓa mantawa da sauye-sauyen da Shugaba Buhari ya kawo sakamakon daƙile cin hanci da rashawa a ɓangaren tallafin man fetur da noma da wutar lantarki ta hanyar cire tallafin ba.

Sai dai cire tallafin ya janyo hauhawar farashin kaya musamman man fetur, wanda gwamnati ta ƙara zuwa naira 151 daga 148, yayin da ‘yan kasuwa su ka ce sai farashin sa ya kai kusan naira 160 a kan kowace lita ɗaya.

Garba Shehu, ya ce tuni ya kamata a ce gwamnatocin baya sun cire tallafin, amma saboda ba su da ƙarfin zuciyar yin hakan sai su ka gaza.

Ya ce za a riƙa tuna Shugaba Buhari a kan yadda ya kawo ci-gaban ƙasa da tattalin arziki ta hanyar daƙile cin hanci da rashawa a ɓangaren kuɗaɗen tallafi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *