Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin sa ta shirya kaddamar da wata gidauniyar tallafa wa matsakaita da kananan ‘yan kasuwa a Nijeriya, ya hanyar tallafa masu da Naira dubu 50 a kowane wata.

Sai dai gwamnati za ta dauki tsauraran matakai wajen zakulo ‘yan kasuwar da za su ci moriyar tallafin, kuma ‘yan kasuwar za su fito ne daga kowanne fanni na kasuwanci.

Shugaban Buhari, ya ce a yunkurin gwamnatin sa na farfado da tattalin arziki a farkon shekara ta 2020, babban bankin Nijeriya ya fitar da Naira Biliyan 100 domin tallafa wa masana’antu.

A cikin Naira Biliyan 100 na tallafin, an raba wa kamfanonin kiwon lafiya da sarrafa magunguna, wanda tuni aka kaddamar da shirye-shirye 37 a kan kudi Naira Biliyan 37.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *