A ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi na ganin an kawo karshen ayyukan ta’addanci da hare-hare a jihar Katsina, Rundunar ‘yan sanda ta jihar ta kama masu aikata laifuffuka da dama.

Waɗanda aka kama sun haɗa da  waɗanda ake zargi da aikata fyade su 140, da ‘yan Bindiga 50, sannan jami’an ta sun kwato shanu sama da  200, da motoci biyu da babura 20.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Sanusi Buba ya bayyana haka, yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Katsina, inda ya ce an samu nasarar kama ɓata-garin ne ta hanyar tattara bayanan sirri.

Ya ce gaya ga kamen da su ka yi, an kwato bindigogi kirar AK 47 guda tara, da bindigogi 20 kirar hannu, da motocin hawa biyu, da babura 20, da shanu 220 da su ka salwanta, da kuma kudi Naira dubu 685.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *