Hukumar Lafiya ta Duniya, ta ce duk da cewa wasu kasashen duniya su na fidda wasu magungunan riga-kafin cutar Korona, za a kai tsakiyar shekara ta 2021 kafin a samu wanda aka tabbatar da ingancin sa.

Mai magana da yawun hukumar Margaret Harris, ta ce hukumar ba ta amince da ingancin wadannan magunguna ba tukunna, dukkan su su na nan a matakin gwaji.

Sai dai tuni har kasar Rasha ta ce ta gama hada maganin riga-kafin cutar har ma ta fara amfani dashi.

Tuni dai Nijeriya ta karbi samfurin maganin, inda Ministan Lafiya Osagie Ehinare ya ce an aika da shi hukumar NAFDAC domin ci-gaba da aiki a kai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *