Tsohon Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita da aka hamɓarar a watan da ya gabata ya bar ƙasar Mali.

Ibrahim Keita ya tafi Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin duba lafiyar sa, sakamakon barazanar da ya ke samu ta shanyewar rabin jiki kamar yadda sojojin ƙasar su ka bayyana.

A halin yaznu dai, sojojin ƙasar su na tattaunawa da ‘yan adawa a ƙasar da ƙungiyoyi masu zaman kan su, a kan yadda za a miƙa mulki ga farar hula.

Sojojin da ke mulki a ƙasar sun bayyana cewa, za su sauka ne nan da shekaru biyu, sai dai shugabannin ƙasashen yammacin Afrika sun ce su na so a yi gaggawar miƙa mulki ga farar hula a ƙasar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *