Gwamnatin Tarayya ta fitar da rahoton cewa, ta kashe naira biliyan 31 wajen yaki da cutar Coronavirus a cikin watanni hudu.

Bayanin hakan ya na kunshe ne a cikin wata takarda da Babban Mai Binciken Kashe Kudade na Kasa Ahmed Idris ya aika wa Kungiyar SERAP da ta nemi sanin adadin kudaden da gwamnatin tarayya ta kashe wajen yaki da cutar Coronavirus.

A ranar 10 Ga Agusta ne, SERAP ta aika wa Ofishin Babban Akanta na kasa wasikar neman sanin kudaden da aka kashe da kuma sanin bayanan adadin wadanda aka raba wa tallafin jin-kai a Nijeriya.

Idris ya maida wa SERAP amsa, inda ya ce an kashe naira biliyan 31 daga ranar 1 Ga Afrilu zuwa 31 Ga Satumba.

Ya ce an tara gudummawa daga jama’a da kamfanoni ta kudi naira biliyan 36 da miliyan 300, an kuma kashe naira biliyan 30 da rabi daga Afrilu zuwa Agusta, sannan a yanzu akwai sauran naira biliyan 5 da miliyan 900 ajiye a Asusun Kudaden yaki da Korona.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *