Hukumomi a Australiya, sun tsawaita dokar kullen annobar korona da tsawon makonni biyu a birnin Melbourne.

Birnin Melbourne dai ya shafe makonni shida ba shiga ba fita, bayan annobar ta yi kukan kura a karo na biyu.

Hukumomin sun ce ko da za a samu sassauci, sai idan an samu raguwar masu kamuwa da cutar a kullum.

Jihar Melbourne ce matattarar annobar korona a ƙasar Australiya, a ɓullar cutar karo na biyu, inda kusan mutane 753 su ka mutu a jihar Melbourne.

A Cikin mutane miliyan 25 da ke ƙasar, mutane dubu 26 ne aka tabbatar sun kamu da cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *