Kwalejin horar da manyan sojoji ta Nijeriya NDA, ta fitar da sunayen waɗanda su ka ci jarrabawar karatun aikin soji tare da sanar da ranar da za a tantance su.

A cikin wata Sanarwa da rajistaran kwalejin Birgediya Janar Ayoola Aboaba ya fitar, ta na ƙunshe da sunayen waɗanda su ka ci jarabawar a dukkan jihohin Nijeriya 36 har da Abuja.

Za a fara tantance kashi na farko na jihohin a ranar Asabar 12 ga watan Satumba na shekara ta 2020, wadanda su ka haɗa da Anambra da Bauchi da Delta da Edo da Ekiti da Enugu da Gombe da Kano da Kaduna da Nasarawa da Ondo da kuma Filato.

Kashi na biyu na jihohin da za a tantance a ranar 26 ga watan Satumba kuma sun haɗa da Abia da Adamawa da Akwa Ibom da Benue da Imo da Katsina da Kogi da Osun da Oyo da Rivers da Yobe da kuma Zamfara.

Jihohin da za a tantance su nea ranar Asabar 10 ga watan Oktoba kuma sun haɗa da Bayelsa da Borno da Cross River da Ebonyi da, Abuja da Jigawa da Kebbi da Kwara da Lagos da Neja da Ogun da Sokoto da kuma Taraba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *