Babban sakataren ma’aikatar ilimi na jihar Anambra Nwabueze Nwankwo, ya ce gwamnatin jihar ta bada umurnin a bude makarantun firamare da sakandare da ke fadin jihar.

Nwankwo ya bayyana da haka ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Awka.

Gwamnatin jihar, ta ce za a bude makarantun na tsawon wata daya domin dalibai su samu rubuta jarabawar su t zangon karshe na shekarar karatu ta 2019 da 2020 daga ranar 14 ga watan Satumba zuwa 23 ga Oktoba.

Nwankwo, ya ce iyaye za su sama wa yara takunkumin fuska da man tsaftace hannu, sannan daliban da ke makarantun kwana za su koma makaranta a karshen mako kafin ranar da gwamnati ta bayyana.

Ya ce koyar da darussa da ake yi wa dalibai ta yanar gizo da gidajen talbijin za su cigaba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *