Matashin awakin da kotun Shari’ar Musulunci ta yanke wa hukuncin kisa a jihar Kano bisa batancin da ya yi wa manzon Allah (SAW) ya daukaka kara.

A karar da lauyan sa Kola Alapini ya shigar a babbar kotun jihar Kano, Sharrif-Aminu ya ce bai amince da hukuncin da kotun shari’ar Musuluncin ta yanke ba.

Lauyan ya ce dokar Penal Code ta shekara ta 2000 ta saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma hakkin bil-Adama.

Lauyoyi da dama dai su na gudun shiga lamarin Yahaya Sharrif, saboda tsoron abin da ka iya biyo baya musamman jiha irin Kano.

Yawancin su su na tsoron matasa na iya kona ofishohin su, ko kuma a kai masu hari ko a kashe su don su na kare mai batanci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *