Gwamnatin Najeriya ta buƙaci gwamnatocin jihohi da shugabannin makarantu masu zaman kansu da su zama cikin shiri domin buɗe makarantu a ƙasar.
Babban jami’in kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa domin yaƙi da annobar korona Sani Aliyu, ya bayyana hakan yayin da kwamitin ke bayar da bayanai kan yanayin cutar a Najeriya.
Ya bayyana cewa makarantun firamare da sakandare da jami’o’i su zama cikin shiri domin akwai yiwuwar buɗe su nan ba da jimawa ba.
Kwamitin shugaban ƙasar ya ce gwamnatocin jihohi su fara tantacewa da tabbatar da duka makarantu a ko wane mataki sun bi ƙa’idojin da aka gindaya na yaƙi da cutar korona da kuma tabbatar da cewa sun samar da wani tsari a ƙasa, da za su iya sa ido ga shirye-shiryen buɗe makarantun.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *