Babban Bankin Nijeriya CBN, ya ba da izinin a shigo da Ton dubu 262 na masara domin rage radadin tsananin karancin abinci da ya addabi al’ummar Nijeriya.

Tuni dai Babban Bankin ya ba wasu kamfanoni uku damar shigo da masarar Nijeriya.

Kamfanonin kuwa sun hada da Wacot and Chi Farms Limited, da Crown Flour Mills, da kuma Premier Feed Mills Company Limited.

Wadannan kamfanonin za su shigo da masarar ne a cikin watannin Agusta da Satumba da kuma Oktoba, kuma in banda su ba a amince ma ko wa ya shigo da kayan abincin ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *