Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ce ƙarin kudin wutar lantarki da aka yi mataki ne da bai dace ba.

A wani sako da ya wallafa a shafin san a Twitter, Atiku ya ce ba ya goyon bayan ƙarin kudin wutar lantarki, yayin da ‘yan Nijeriya ke murmurewa daga raɗaɗin kullen korona.

 Ya ce ‘yan N   ijeriya ƙarfafawa su ke buƙata ba wai yin watsi da ƙalubalen da su ke fuskanta ba.

Atiku Abubakar ya kara da cewa, ‘yan Nijeriya da dama sun shafe tsawon watanni babu kuɗaɗen shiga kuma ba laifin su ne ba, don haka ya ce ƙarin kudin wutar bai dace ba kuma  gurguwar shawara ce.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *