Fadar shugaban kasa ta ce shugaba Buhari ya bada umurnin fitar da kaya daga rumbun adana kayayyakin abinci, domin rage tsadar kayayyakin a fadin Najeriya.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Shehu ya ce shugaba Buhari ya nuna damuwarsa kan hauhawan farashin kayan abinci a wannan lokaci da cutar korona ta jefa tattalin arzikin kasashen duniya cikin mawuyacin hali.

Shugaba Buhari ya kuma ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatinsa za ta dauki wasu matakai da za su taimaka wajen kawo saukin rayuwa musamman kan farashin kayayyakin.

Sannan ya nuna damuwa kan yadda wasu ‘yan kasuwa ke amfani da wannan lokaci da ake ciki wajen kara tsadar kayayyaki da zummar samun kazamar riba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *