Mai martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta jihar Naija su gaggauta gyaran hanyoyin jihar Naija, wanda a cewarsa jiha ce mai matukar muhimmanci a Arewacin Najeriya.

Basaraken wanda shine shugaban majalisar sarakuna na jihar Kano, ya mika bukatar ce a wajen bikin daren al’adu da Etsu na Nupe ya shirya na musamman domin karrama ziyarar sarkin na Kano.

Bayero, ya ce janyo hankalin gwamnatocin ya zama wajibi, duba da irin halin da hanyoyin jihar suke ciki a yanzu.

Ya kara da cewa gyaran hanyoyin zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki, inganta rayuwa da kuma saukakawa masu ababen hawa domin su kai duk inda suka son zuwa.

Bayero ya ce jihar ta Naija na da matukar muhimmanci ga Najeriya ta fuskar tattalin arziki da siyasa, saboda yankin da take.

Sannan ya yabawa dangantakar dake tsakanin jihohin biyu, yana mai cewa sun amfana ta bangarori da dama musamman mutuntakar dake tsakanin masarautun biyu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *