Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya gana da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a fadar shugaban kasa dake Abuja.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan ganawar tasu, gwamnan jihar ta Kano ya ce tattaunawar ta su ta maida hankali ne kan tsaro da ilimi.

Ya ce ya bayyanawa mataimakin shugaban kasan irin kalubale da jihar ke fuskanta da suka hada da garkuwa da mutane, satar shanu, fashi da makami, da sauran su.

Ya ce jami’an soji na aiki ba dare ba rana dan ganin sun fatattaki ‘yan ta’adda daga dajin Falgore dake karamar hukumar Doguwa a jihar.

Ganduje ya kara da cewa mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya nuna farin cikinsa da rahoton da ya samu kan nasarori a yaki da ‘yan ta’addan da suka addabi yankin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *