Nigeria’s President Muhammadu Buhari (L) shakes hands with India’s Prime Minister Narendra Modi during their meeting at the India-Africa Forum Summit in New Delhi on October 28, 2015. The event, postponed since December over the Ebola crisis, is the first under Indian Prime Minister Narendra Modi and is the biggest gathering of foreign dignitaries in the country since 1983 with some 1,000 delegates. AFP PHOTO / PRAKASH SINGH (Photo credit should read PRAKASH SINGH/AFP/Getty Images)

Gwamnatin tarayya da kasar India sun kara karfafa dangantakar dake tsakaninsu musamman a bangaren farfado da tattalin arziki, kasuwanci, zuba jari, tsaro da sauran su.

Bayanin hakan ne kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun Ministan kula da harkokin kasashen ketare Geoffrey Onyeama, da takwaransa na kasar India S. Jaishanka.

Kasashen biyu sun ce bayan amfani da irin nasararo da aka samu a yarjejeniyar da ke tsakanin kasashen biyu, suna da tabbacin fadada yarjejeniyar zai sa a samu nasarori a abubuwan da suka sanya a gaba.

Ministocin biyu sun kuma bada sanarwar cewa akwai taron da zasu gudanar na hadin gwiwa kan tsaro a cikin wannan shekarar a babban birnin tarayya Abuja.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *