Hukumar hana sha da fataucin kwayoyi ta Najeriya NDLEA, reshen jihar Kogi ta lalata gonar tabar wiwi a Okula dake karamar hukumar Ofu a jihar.

Kwamandan hukumar a jihar Alfred Adewumi, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Okula, jim kadan bayan lalata gonar.

Adewumi ya nuna takaicinsa kan yadda ake ci gaba da samun yawaitar masu noma tabar wiwi a fadin jihar.

Ya kara da cewa bayanan sirri da suka samu ya sa sun kama wani mai suna Clement Akor dan kimanin shekaru 42 wanda ake kyautata zaton gonarsa ne a karamar hukumar Ankpa dake jihar.

Adewumi ya ce wannan na zuwa ne kwanaki 3 bayan kama wasu mutane da suka hada da Enduarance Samson, da Abah Sunday da tabar wiwi mai nauyin kilogram 36.

Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da bin manoman tabar wiwi da kuma masu ta’ammuli da ita har sai ta tabbatar da an daina ta’ammuli da ita a fadin jihar baki daya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *