Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta ce ta gurfanar da shugabar gidauniyar kula da tare da tallafawa mabukata Aisha Alkali Wakil da aka fi sani da Mama Boko Haram.

Hukumar ta gurfanar da Mama Boko Haram ne a babbar kotun jihar Borno dake Maiduguri karkashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Kumaliya.

Hukumar na tuhumar Mama Boko Haram ne da bada bayanan karya, da kuma yin almundahanan naira milliyan 6. 

A wata sanarwa da ta fito ta hannun jami’in yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Dele Oyewale, ya ce a zaman kotun Mai Shari’a Kumaliya ta bukaci a karantawa wadanda aka shigar karar tuhume-tuhumen da ake yi mata.

Sai dai bayan sauraron tuhume-tuhumen, sun ki amincewa da aikata laifukkan da ake zarginsu da aikatawa, inda wasu daga cikin lauyoyinsu suka bukaci kotun ta dage shari’ar domin basu damar kare kawunansu a gaba.

A karshe kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga wannan watan na Satumba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *