Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da kafa ranar 1 ga watan Nuwamba a matsayin ranar matasa ta Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan amincewar kwamitin da aka kafa domin duba ranar da ya kamata a fitar a matsayin ranar matasan a cikin wata takarda ta hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari.

An kafa kwamitin ne domin duba takardar da ministan kula da matasa da ci gaban wasanni Sunday Dare, ya gabatar.

Za a yi amfani da ranar ta 1 ga watan Nuwamban ne domin wayar da kai kan irin matsalolin dake damun matasa, ta hanyar shirya tarurruka da gangami.

Sanarwar da aka fitar ta bukaci ministan kula da harkokin matasa da wasanni ya fitar da takardan Kwamitin farfado da tattalin arziki na jihohi kan irin shirin da suke dashi akan ranar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *