Wata kotun majistire da ke Gabasawa a kan titin Taiwo Road a garin Kaduna, ta bada umarnin tsare Mrs. Yemi Awolola a gidan yari, bisa zargin ta da azabtar da ‘yar aikin ta mai shekaru 14 mai suna Princess Michael zuwa ranar 10 ga watan Satumba kafin a mika ta zuwa babbar kotu shari’ar.

Bayan karanta kara ga wadanda ake zargin, Alkalin kotun Benjamin Hassan, ya ce sakamakon dangantaka da sashe na 207 na kundin tsarin mulkin Nijeriya a kan shari’ar, babbar kotu ce kawai za ta iya yanke hukunci a kan wannan shari’a.

 Ya ce kotun ta ba yara biyu da ke da alaka da lamarin beli ne saboda kananan yara ne, da kuma ikirarin da cibiyar gyaran hali ta yi cewa ba ta da wajen da za ta ajiye su.

A ranar 3 ga watan Yuli ne, Mrs Yemi Awolola ta sa ‘yar ta da wata ‘yar aiki suka rike kafafuwan Princess Michael, sannan ta yi amfani da ashana ta kona gaban ta da mazaunan ta saboda ta na zargin ta daukar mata kayan abinci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *