Shugaban Hukumar Sadarwa ta Nijeriya Umar Danbatta, ya ce masu amfani da layin wayar salula a Nijeriya sun ƙaru zuwa miliyan 199 da dubu 300.

Ya ce an samu ƙaruwar ne daga miliyan 184 a watan Disamba na shekara ta 2019 zuwa Mayu na shekara ta 2020.

Dambatta ya bayyana haka ne, yayin miƙa lamunin kuɗi da hukumar ta ba wasu cibiyoyin sadarwa biyu da za su gudanar da bincike a kan annobar korona.

Ya ce masu amfani da yanar gizo sun ƙaru a tsawon wannan lokacin daga miliyan 126 zuwa miliyan 147 da dubu 100, yayin da masu sayen layin intanet a dunƙule su ka ƙaru daga miliyan 72 zuwa miliyan 80 da dubu 200.

Farfesan ya kara da cewa, irin wannan bincike zai taimaka wajen samar da yiwuwar gudanar da tarurruka ta yanar gizo da za su riƙa samar da tazara tsakanin mutane.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *