Gwamnan jihar Enugu Ifeanyi Ugwanyi, ya yi kira ga ‘yan kungiyar masu rajin kafa kasar Biyafara su maida makaman da su ka kwace daga hannun jami’an yan sanda.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 23 ga watan Agusta na shekara ta 2020, an yi rikici tsakanin jami’an tsaro na farin kaya DSS da matasan IPOB masu zanga-zanga, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar jami’an hukumar DSS biyu.

Haka kuma, a ranar 28 ga watan, wasu matasa sun kai farmaki ofishin ‘yan sanda na tashar jirgin kasa da ke Ogui, da kuma ranar 30 ga wata a ofishin ‘yan sanda na Abapka inda su ka kwashe makamai.

Gwamnan ya ce su maida makaman da su ka kwace wajen sarakunan gargajiyar su saboda a maida wa hukuma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *