Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Femi Fani-Kayode, ya yi barazanar maka jaridar Daily Trust kotu, tare da neman diyyar naira bilyan 6 saboda abin da ya kira bata ma shi suna da ya ce jaridar ta yi.

Femi Fani-Kayode, zai kuma hada da wani marubuci mai suna Iliyasu Gadu dangane da batancin da ya ce ya yi ma shi a cikin jaridar.

Zazzafan rubutun da ya harzuka Fani-Kayode dai, sun biyo bayan tozarta wakilin jaridar mai suna Charles Eyo da yay i a birnin Calabar kwanan baya.

Tsohon ministan dai  ya rika surfa wa dan jaridar zagi, don kawai ya nemi jin wanda ke daukar nauyin rangadin jihohin da Fani-Kayode ke yi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *