Fadar Shugaban kasa ta ce ayyuka da tsare-tsaren da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi a yanzu sun bambanta da alkawurran da ya yi a lokacin yakin zabe.

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu, ya ce abubuwa mafi muhimmanci da gwamnati ta sa gaba, wadanda su ka bambanta da alkawarin da aka yi a lokacin yakin neman zabe, sun dogara ne ga irin karfi da nauyin da aljihun gwamnati ke da shi.

Ya ce babu wata gwamnatin da za ta hau mulki har wa’adi biyu, kuma ta tsaya kawai a kan alkawurran da ta yi wa jama’a kafin ta hau mulki.

Bayan ya kada tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a zaben shekara ta 2015, Shugaba Buhari ya yi alkawarin samar da tsaro da hana cin hanci da rashawa da kuma inganta tattalin arziki. Garba Shehu, ya ce tawayar da tattalin arziki ya samu a Nijeriya da ma duniya baki daya saboda annobar Korona, ya na bukatar jajircewa wajen ganin an maida shi a kan sahihiyar hanyar bijiro da tsare-tsaren inganta tattalin arziki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *