Kungiyar masu gidajen mai masu zaman kan su ta kasa IPMAN, ta umarci ‘ya’yanta su kara kudin farashin mai zuwa Naira 162 a kan kowace lita.

IPMAN ta ce ta dauki matakin ne sakamakon karin kudin mai da gwamantin tarayya ta yi zuwa Naira 151 da kobo 56.

A cikin wata sanarwa da reshen kungiyar na shiyyar kudu maso yamma ya fitar, ta ce ba su da wani zabi illa su kara kudin man domin gudun kada su yi asara.

Shugaban kungiyar IPMAN reshen jihar Kano mai kula da wasu jihohin arewacin Nijeriya Bashar Dan Malam, ya ce dole ne su yi karin, domin cike gibin karin da za su samu daga wajen da su ke sayo man fetur sakamakon matakin gwamnati na maida litar fetur Naira 151 da kobo 56.

Wannan gai shi ne karo na uku da gwamnati ke sauya farashin mai a ‘yan watannin baya-bayan nan, sai dai sabanin wasu okutan da ake rage farashin, karin man na wannan karon shi ne mafi yawa a baya-bayan nan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *