Mai martaba Shehun Borno Abubakar Garbai Elkanemi, ya ce ‘yan ta’addan Boko Haram sun kashe wasu sarakunan gargajiya 13 a masarautarsa.

Basaraken ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakwancin tawagar kwamitin ayyuka na musamman na majalisar dattawa karkashin jagorancin dan majalisa Abubakar Yusuf.

Ya ce ayyukan ta’addanci da aka dauki tsawon shekaru ana yaki dashi yayi sanadiyyar tserewar mutane da dama daga garuruwansu, wanda yanzu haka ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Sannan ya bukaci gwamnatin tarayya ta tura da karin kudade hukumar kula da yankin arewa maso gabas, duba da irin wahalhalu da kungiyar Boko Haram ta jefa al’ummar jihar a ciki.

Ya kuma yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ‘yan majalisar dokoki bisa amincewa da kafa hukumar kula da yankin arewa maso gabas domin magance matsalolin yankin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *