Babban sufetan ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya bukaci kungiyoyi masu zaman kansu su karfafa hadin gwiwa dake tsakanin su da hukumomin tsaro gabannin zabubbukan jihohi Edo da Ondo.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai da hulda da jama’a Frank Mba ya fitar a Abuja, inda ya ce Mohammed ya yi kiran ne a wani taron kwana da kungiyoyi masu zaman kansu.

Ya ce ya yi kiran ne domin karfafawa aikin dan sanda tare da tabbatar da nasarori a zabubbukan da za a gudanar ranakun 19 ga watan Satumba da 10 ga watan Oktoba a jihohin biyu.

Ya ce kungiyoyi masu zaman kansu na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen tabbatar da sahihancin zabe da kuma dorewar mulkin dimokradiyya a fadin Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *